A dai dai lokacin da ake shiryen-shiryen biki mika mulki ga sabuwar gwamnati tawagar zababben shugaban kasar Kenya, ta hana kafafen yada labaran cikin gida yada bikin rantsar da sabon shugaban kasar, tare da ba da haƙƙin watsa shirye-shirye na musamman ga Multichoice Kenya Limited, Gammayyar ƙungiyar rukunin kafafen talbijin dake da asali daga Afirka ta Kudu.
BBC ta ruwaito cewa, Sai dai kungiyar ma’aikata kafafen yada labarai na kasar Kenya wago KBC, bai da wani karfi a kungiyar ta Multichoice Kenya Limited.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamna Bagudu Ya Baiwa Hukumar Hisba Naira Milliyan 100
Haka kuma, kafofin yada labaran kasar za su karɓi kwangilar yada shirye-shiryen ne kai tsaye daka kungiyar..
Rahotanni sun nuna cewa ba’a bayyana cikakkun bayanai kan lamarin ba, amma a lokacin bikin rantsar da shugaban kasar a baya, kafafen yada labaran cikin gida sun samu cimma matsaya da gwamnati ba tare da wani mai shiga tsakani ba.
Sanarwar da kwamitin ya fitar dai ta fuskanci ce-cekucen yan jarida da kungiyoyin yada labaran kasar, inda babbar jaridar Daily Nation dake aiki a kasar ta Kenya ta zargi zababben shugaban kasar da barnatar da damar amfani da kayayyakin cikin gida.
A cikin wani rahoto data fitar a yau litinin jaridar Daily Nation ta rubuta cewa, abinda kwamitin yayi na bayar da damar ga kafofin yada labaran kasashen waje alhakin gudanar da ayyukan gwamnati abu ne da bai dace ba.
Haka kuma kwamitin yada labarai na Mista Ruto ya kare kansa kan wannan zargi, yana mai cewa dan kwangilar zai ba da abinda ake bukata.
Kwamitin kuma har ila yau, ya zargi kafofin yada labaran cikin gida da nuna son kai ga Mista Ruto, tare da nuna rashin jin dadinsa kan kin yada ayyukansa na yakin neman zaben.
A WANI LABARIN KUMA: Yan sanda Sun Bindige Wani Da Ake Zargun Mai Garkuwa Da Mutane Ne
Jami’an hukumar ‘yan sanda reshen jihar Edo sun kashe wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne a yayin wani artabu da ‘yan sanda a jihar Edo.
Daily Trust ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a dajin Ughiole da ke karamar hukumar Etsako ta Yamma a jihar a ranar Lahadi.