Mutane shida da ake fargabar sun mutu a wani harin da aka kai cikin dare a shingen binciken ‘yan sandan Jihar Koros Riba sun rigamu Gidan Gaskiya.
Kimanin ƴan sanda shida da soja ɗaya ake tsammani wasu gungun ƴan bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka kashe waɗanda suka kai hari kan wasu shingen binciken ababen hawa a gefen Obubra na babbar hanyar Calabar-Ikom a daren Talata.
Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda, ASP Irene Ugbo ya tabbatar da faruwar lamarin amma ya yi ikirarin cewa’ yan sanda biyu da soja daya ne suka ji rauni.
Ta ce an sake aiwatar da tsaro a yankin kuma akwai farauta Ta musamman da suka tura jami’an su kan maharan wadanda daga baya suka yi watsi da motarsu suka gudu zuwa daji lokacin da suke artabun musayar wuta da jami’an mu, Inji shi.
Kakakin rundunar ‘yan sandar ya kuma yi ikirarin cewa bindigogin yan sanda biyu ne maharan suka tafi da su.
Majiyoyi a karamar hukumar Obubra sun bayyana cewa lamarin ya faru ne “da misalin karfe 11 na daren ranar Talata tare da Ofotura inda aka harbe jami’ai 2 aka kuma kashe wasu jami’ai 4 su ma a filin binciken na Oyadama.
An yi amannar cewa maharan sun fara ne daga yankin Nko na babbar hanyar da ke kan shingen bincike zuwa cikin Obubra. Maharan sun zo ne cikin wata motar kasuwanci da ake zargin an kwace ta ne don yin aikin kuma an watsar da ita a shingen binciken yayin da sukaji wuta daga jami’an mu wanda hakan ya Tilasta musu guduwa cikin Daji, Inji shi.
Jaridar The Nation ta kara da cewa maharan sun kai hari har zuwa shingayen bincike uku a kan babbar hanya kafin su hadu da shingen binciken da Sojojin suka kafa.
“Sojojin ne suka fi karfin su kuma suka gudu zuwa cikin daji. Wani Soja daya ne ya ji mummunan rauni kuma ake tsammanin ya mutu amma an kashe ’yan sanda hudu, an dauki bindigoginsu kuma da yawa daga cikinsu da suka samu raunuka na karbar kulawar likita a safiyar yau, kamar yadda majiyarmu ta ce.
Wannan harin na zuwa ne kusan mako guda bayan wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun harbe wasu’ yan sanda hudu a wani shingen binciken ababan hawa da ke kan hanyar Idundu a wajen karamar hukumar Calabar.
Bayan harin da aka kaiwa ‘yan sanda hudu a Idundu, Kwamishinan’ yan sanda CP Sikiru Akande ya lura cewa manufar ita ce rage kokarin ‘yan sanda amma maharan ba za su yi nasara ba. “Za mu mayar da martani. Kuma za mu kama dukkan su, Inji shi.
Ya zuwa lokacin Haɗa wannan rahoton, rundunar ‘yan sanda tare da jami’an tsaro na farautar waɗannan Miyagu a cikin daji da kuma yankin Obubra inda maharan suka gudu zuwa can.