Rahotanni da suke fitowa daga jihar, Kwamishinan lura da harkokin tsaron cikin gida, Samuel Aruwan a wata sanarwa da ya fitar ya tabbatar da cewa; gwamnatin Kaduna ta haramta kafa shigen ‘yan sanda a manyan titunan Kaduna zuwa Abuja, da kuma Kaduna zuwa Zariya, tare da kuma Kaduna zuwa Birnin Gwari
Sanarwar ta ci gaba da cewa; daga yanzu duk wani shingen ‘yan sanda ko Sojoji a manyan titunan Kaduna-Abuja, Kaduna-Zaria, Kaduna-Birnin Gwari ya haramta. Ya kara da cewa; “duk shingen da jami’an tsaro suka kafa a wannan tituna karya doka ne.” In ji shi.
Sannan ya yi kira ga matafiya da su sanar da gwamnati duk inda suka ga irin haka domin ya haramta.
Titunan Kaduna zuwa Abuja, Kaduna zuwa Zariya da kuma Kaduna zuwa Birnin Gwari sun yi kazamin suna wajen hare-hare, Fashi da Makami da kuma garkuwa da mutane domin kudin fansa.