Gwamnatin Kano ta haramta sayar da sinadarin dan tsami da danginsa a fadin jihar baki daya, biyo bayan wata cuta da ake zargin sinadarin ya haifar.
Shugaban hukumar kare hakkin masu sayan kayayyaki Baffa Babba Dan Agundi ne ya tabbatar da hakan.
Baffa ya ce bincike ya nuna cewa wannan sinadari da ake hada kayan shaye-shaye da su da yawansu lokacin ingancinsu ya kare, don haka babu mamaki dan an ce suna cutar da masu amfani da su.
Ya kara da cewa sakamakon binciken da suke yi sun kama buhu 583 na irin wadannan sinadirai da wa’adinsu ya kare.