A ranar Lahadi ne aka harbe wani dan takarar a zaben kananan hukumomin jihar Kaduna da ya gabata, Steven Inuwa a Abuja.
Inuwa ya tsaya takara a karkashin inuwar jam’iyyar PDP.
Haka kuma wasu ‘yan bindiga da ba a tantance ba sun kashe abokinsa Earnest Agatha, inda suka yi harbin kan motar da suke tukawa a kusa da yankin Zuma da ke wajen garin Bwari.
Wani makusancin marigayin, John Alpha, a lokacin da yake zantawa da manema labarai jiya, ya ce Agatha da ke tuka motar ya mutu nan take, yayin da aka garzaya da dan siyasar zuwa babban asibitin Bwari, inda aka tabbatar da rasuwarsa da isar shi.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan FCT, DSP Josephine Adah, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta kara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.