Alamka Dominic Usman (cashman), wani Dan takarar shugabancin Jam’iyyar APC ne, na Karamar hukumar Kachia, inda aka sami wani Dan bindiga dadi ya busa masa alburusai a Jahar Benue. Jaridar Daily trust ta wallafa a shafinta
Alhaji Ahmed Tijjani Sulaiman, shugaban jam’iyyar ta APC ta Karamar hukumar Kachia, yace an harbe Dominic a wani guri a Jahar Benue.
Alhaji Ahmed Tijjani Sulaiman, yace Dominic mutum ne wanda jam’iyyar ta APC tayi amanna da shi a karamar hukumar, ya gamu da ajalinsa ne inda yake kokarin ziyarar iyalansa dake Jahar Benue, bai sani ba ashe zai gamu da ajalinsa ne.
KARANTA:- YANZU-YANZU: Kotun Koli ta kori ƙarar da aka shigar kan rushe zaben Ondo
Alhaji Suleiman yace “Tun da dai ya bar Kaduna da shirin zuwa Benue a ranar Alhamis ba muji daga gareshi ba, sai dai muka sami labarin an sheke shi”.
Har dai izuwa lokacin da ya mutu, shine tsayayyen Dan takarar shugabancin Jam’iyyar APC a karamar hukumar ta Kachia a Jahar Kaduna.
Inda za’a gudanar da zaben a sha hudu ga watan Agusta na wannan shekarar.
Za’a rufe Usman Dominic a gobe Alhamis, wanda yayi dai-dai da ashirin da tara ga watan July.
A wani labarin Hukumar SON ta yi murna da nasarorin da take samu wajan dakile kayan bogi
Mista Faruk Salim, Darakta na hukumar dake yaki da gurbatattun kaya watau SON, yace hukumar na yin nasara sosai wajan yaki akan harka da gurbatattun kaya.
Mista Faruk Salim, ya bayyana hakane a wani taron karawa juna sani da aka gudanar a garin Legas.
Taron dai, an tattauna akan yadda za’a samar da sabbin hanyoyi wajan inganta kayan masarufi na yau da kullun.
Mista Salim ya ce, rahotanni da suke zuwa daga yan kasuwa da masu hannun jari yana nuna musu cewar akwai cigaba wajan samar da ingantattun kaya.
A lokacin da ake masa korafi kan sayan kaya ta yanar gizo, cewa yayi ya kamata masu sayen kaya ta yanar gizo su dinka tuntubar hukumar domin sayen kaya ta yanar gizo abune mai cike da rudani.
Ya cigaba da cewa akwai ofisoshi da dama a cikin kasar nan, kuna iya kawo mana kayan tare da katin shaidar sayen kayan don tabbatar da ingancin su.
Mista Salim, ya bayyana cewa akwai taro na karawa juna sani kan yanar gizo da za’a cigaba da aiwatar wa don wayarma mutane kai.
Daraktan ya ce akwai wasu ayyuka 658 da hukumar za ta gudanar kamin karshen shekarar 2023.
Daraktan ya cigaba da cewa wannan ayyukan za su taimakawa gwamnatin tarayya wajan habbaka tattalin arziqin kasar nan.
Comments 1