By Ishaq Dabai
An harbe wani makiyayi mai shekaru 18 har lahira a Kafigana da ke gundumar Jebu ta karamar hukumar Bassa a jihar Filato, wannan mummunan lamari ya faru ne da yammacin ranar Lahadi.
Shugaban kungiyar ci gaban Fulani ta Najeriya GAFDAN, Garba Abdullahi Muhammed, wanda ya tabbatar ya shaida wa manema labarai cewa an kashe mamacin ne yayin da yake kiwon shanu a yankin.
Yace, “Yana tafiya ne kawai yadda ya saba tafiya sai‘ yan bindigar suka kutsa cikin yankin suka harbe shi a wuyansa inda yayi sana diyyar mutuwar sa har lahira.Har yaushe za a daina kashe makiyaya ta wannan hanyar ba tare da aikata wani laifi ba? Suna kashe shanunmu da makiyayanmu yadda suke so.An kashe shanu sama da ashirin a wannan watan.
Mun riga mun sanar da Hedikwatar ‘Yan Sanda da ke Bassa.An kwashe marigayin tare da ‘yan sanda, Muna kira ga jami’an tsaro dasu gaggauta yin kira ga wadanda ke aikata wannan aika aikar Ba za a iya kashe mu ba kawai ba tare da wata kariya ba, ”in ji shugaban.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Ubah Gabriel, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike don kamo wadanda suka kai harin.sannan yace duk kabilun Fulani da Irigwe sukan zargi juna kan hare hare da kashe kashe da dama a kauyukan karamar hukumar Bassa.