By Abbas Yakubu Yaura
Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe wani Reverend Father, mai suna Luke Adeleke mai shekaru 38 a duniya yayin da yake kan hanyar sa ta dawowa daga hidimar coci a jajibirin Kirsimeti a jihar Ogun.
Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun kai wa malamin hari a Ogunmakin dake karamar hukumar Obafemi-Owode a jihar inda suka harbe shi har lahira.
“Yan bindiga sun harbe Reverend Father Luke Adeleke, mai shekaru 38, a lokacin da yake dawowa daga wurin ibada a jajibirin Kirsimeti,” in ji wata majiya.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, mataimakin Sufeton ‘yan sandan ya tabbatar da faruwar lamarin.
Oyeyemi yace lamarin ya faru ne a Ogunmakin ba a Odeda ba, kamar yadda ake yadawa a shafukan sada zumunta.
Sannan Yace ‘yan bindigar sun yi musayar wuta da ‘yan sanda a yankin inda suka tsere da raunukan harbin bindiga.
Ya kara da cewa, “Hakan ya faru ne a Ogunmakin dake karamar hukumar Obafemi-Owode a jihar ranar Juma’a.
Kokarin jin martani daga Ofishin Jakadancin Katolika a jihar bai yi nasara ba har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto.