Shugaban Kungiyar ‘yan jarida ta kasa, NUJ, Chris Isiguzo ya yaba wa Gwamnatin Tarayya kan kokarinta na yaki da ayyukan ta’addancin kungiyar Boko Haram a Arewa maso Gabashin Nijeriya.
Isiguzo ya yi yabon ne a Gombe ranar Asabar yayin da yake hira da manema labarai.
Ya ce, yaje jihar ne don tattaunawa da ‘yan jarida saboda tattara batutuwan Kudurin Inganta Aikin Jarida, wanda ake sa ran zai magance matsalolin da manema labarai suke fama ita a Nijeriya.
Ya ce, tabbas gaskiya ne yanzu Boko Haram ba ta karfi saboda ya ga zaman lafiya ya samu a wurare yayin da yake yawo a cikin yankin Arewa maso Gabas din kasar.