Farfesa Razaq Abubakre, tsohon shugaban Jami’ar Al-Hikmah University, dake Ilorin, ya jinjinawa shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa kafa Kwalejin Ilimi ta gwamnatin tarayya a garin Iwo dake jihar Osun.
Abubakre, ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a birnin tarayya Abuja a yau Alhamis.
Sanarwa wanda Sulayman El-Mavericky ya sanyawa hannu a madadin kungiyar al’ummar Ileri-Oluwa dake Iwoland, wanda Abubakre ke yi jagoranci.
Sannan Farfesan ya jinjinawa Ministan ilimi, Adamu Adamu, Gwamnan Jihar, Isiaka Oyetola bisa zabar garin na Iwo wajen kai Kwalejin ilimin.