An yi ta harbe-harbe da dama a wurin da fashewar ta afku a unguwar Sabongari da ke Kano a safiyar ranar Talata.
Jami’an tsaro ne suka yi harbin don tarwatsa jama’ar da Yan uwansu suka rasa rayukansu a wurin.
Tun da farko dai wasu daga cikin matasan sun far wa sojojin da duwatsu amma an shawo kan lamarin.
Sai dai yayin da wakilin Jaridar Daily Trust ya halarci wurin, kanewa idanunsa yadda jami’an tsaro sukai ta yin harbin iska domin tarwatsa jama’a.
Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa yayin da ake ci gaba da aikin ceto, wasu ‘batagari sun fara amfani da lamarin wajen kutsawa cikin shaguna da gidajen mutane.
A halin da ake ciki kuma, ana ci gaba da gudanar da aikin kwashe mutanen har zuwa lokacin hada wannan rahoto inda aka tabbatar da mutuwar mutane hudu.
A wani labarin Kuma na daban.
Buhari ya yiwa Ƙasar nan duk abinda ya kamata — Wani Ɗan Majalisa a Katsina
Ɗan Majalisar Wakilai Mai Wakiltar Ƙaramar Hukumar Funtua/Ɗandume a Jahar Katsina Muntari Dandutse yace Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari yayi aiki mai kyau a matsayin sa na Shugaba.
Ya bayyana cewa wannan dalilin ne ya sanya Jam’iyyar APC keda ƙarfi a Katsina, duk da Canja Sheƙa da ɗaya daga cikin Sanatocin Jahar.
Dandutse yayi magana akan Ɗan Majalisa Mai Wakiltar Katsina ta Arewa inda Buhari ya fito, Sanata Ahmed Kaita wanda a watan Afrilu ya sanar da canja sheƙar sa daga Jam’iyyar APC Mai Mulki zuwa Jam’iyyar PDP.
Dandutse yayi zargin cewa Babba Kaita da sauran su da ke Son kawo tangarɗa, suna yi ne domin cimma muradun su, kuma ƴan siyasa ne da basa bin Dokoki da sharuɗɗa.
Ɗan Majalisar ya bayyana haka a Abuja, bayan ya miƙa Fom ɗin sa na Takara domin neman Takarar APC a Kujerar Sanata a Babban zabe na Shekarar 2023.
Ɗan Majalisar yace domin ƴan Najeriya su ciyar da Ƙasar su a gaba, suna buƙatar jefar da bambance-bambancen kabilanci da Addini.