Tsananin karar Tarwatsewar wani Abu ya dugunzuma hankalin makwafta barikin soji na Ebrutu a Garin Calabar, babban birnin jihar Cross River.
Har kawo hada wannan rahoton ba a san abin da ya haddasa fashewar ba, amma rufin gine -ginen da ke makwabtaka da kusa da barikin sun rushe, kuma gilashin taga a wasu gine -ginen sun tarwatse
Wani Mazaunin yankin, Mai suna Ekong James, ya shaida wa jaridar Vanguard cewa, lamarin ya shafi rufin gine -ginen rukunin gidajen da yake zaune.
“fashewa na ƙarshe ya faru ne sa’o’i biyu da suka gabata, kuma ina da hotunan rufin da fashewar ta lalata. Babu wanda ya gaya mana abin da ya faru ”a cewar shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Satar Kaddarorin Coci: Kotu ta daure wani na tsawon watanni 6 a Legas
” Kyaftin Aluko, jami’ar hulda da jama’a na rundunar soji shiyar jihar bata dauki kiran wayar da aka yi mata ba, ko Maido da Marti kan sakon kartakkwana ba,” inji jaridar Vanguard.
Comments 1