An ji karar harbe-harbe a barikin soji da dama a kasar Burkina Faso a ranar Lahadi, ciki har da biyu a Ouagadougou babban birnin kasar, kamar yadda majiyoyin soji da mazauna yankin suka shaida wa AFP.
“Tun da karfe 1 na safe, aka fara jin karar harbe-harbe a nan Gounghin dake fitowa daga sansanin Sangoule Lamizana,” in ji wani soja a gundumar da ke wajen yammacin Ouagadougou.
Mazauna yankin, wadanda suka nuna fargaba, sun kuma yi magana game da “harbe harben mai tsanani”.
An kuma ji karar harbe-harbe a wani sansanin sojin Baby Sy, da ke kudancin babban birnin kasar, da kuma wani sansanin sojin sama dake kusa da filin jirgin, in ji majiyoyin sojin.
An kuma yi ta harbe-harbe a bariki a garuruwan Kaya da Ouahigouya da ke arewacin kasar, kamar yadda mazauna wurin suka shaida wa AFP.
Musayar wutar na zuwa ne kwana guda bayan ‘yan sanda sun kame mutane da dama a zanga-zangar adawa da gazawar gwamnati wajen dakile tashe-tashen hankulan masu jihadi da suka addabi kasar da ke yammacin Afirka.
Majiyoyin tsaro sun ce an kashe sojoji biyu a arewacin kasar a lokacin zanga-zangar da hukumomi suka haramta a farkon mako.
A garin Kaya, mazauna yankin sun shaida wa AFP cewa masu zanga-zangar sun mamaye hedikwatar jam’iyyar mai mulki.
Kungiyoyin da ke da alaka da Al-Qaeda da kuma kungiyar IS sun addabi al’ummar yankin Sahel da ba ta da sakat tun shekara ta 2015, inda suka kashe mutane kusan 2,000 a cewar wani kididdiga na AFP.
Comments 1