Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin kaddamar da tallafin Taki ga manoma dubu uku da iftila’in ambaliya ya shafa a gaba daya jahohin kasar nan. Kamar yadda Jaridar Tvcnews ta wallafa a shafinta
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari shine dai Jagoran gidauniyar samar da abinci, wanda mataimakinsa gwamnan Jahar Kebbi Atiku Bagudu, ya wakilce shi a yayin kaddamar da tallafin.
Ambaliyar dai ta zamo sanadiyyar rushe gidaje da gonakin jama’a gami da salwantar abubuwan daban-daban.
KARANTA:- Kasar Senegal na neman taimakon Nigeria wajan samar da kamfanin Mai da iskar gas
Buhari yace an amince da bada tallafin ne don ya rage radadin asarar da manoma suka tafka a lokacin da ambaliyar ta auku.
Shugaba Buhari yace wannan ya zo ne karkashin hukumar samar da tsaron abinci dake karkashin jagorancin nasa.
Yayi kira ga Yan Najeriya da su sanya ido wajan tabbatar da cewa tallafin ya isa ga hannun talakawa da wadanda abun ya shafa.
Kamar yadda yace ya kamata kungiyoyi ma su zaman kansu, da kafafen watsa labarai su taimaka don ganin kowa ya sami tallafin.
Daga cikin kayan da za’a rarraba wajan tallafin sun hada da kayan feshi, masara, irin shuka daban-daban, maganin feshi da sauran kayayyaki noma daban-daban.
A wani labarin
Rikicin Plateau: mutane 17 sun mutu inda aka rushe gidaje 85
Kwamishinan Ƴansandan Jahar Plateau Mista Edward Egbuka, ya bayyana cewa mutane 17 sun rasa rayukansu a inda aka kone gidaje 85 bayan barkewar rikici a kananan hukumomi Bassa da Riyom dake Jahar.
Mista Edward Egbuka, ya bayyana hakane bayan sun kammala ganawa da juna akan matsalar tsaro a gidan gwamnati dake Jos.
Yace akwai rikici da ya barke a Jebbu Miango Karamar hukumar Bassa inda aka hallaka mutane biyar, sannan mutane sha biyu suka mutu rikicin da ya barke a Tambora Karamar hukumar Riyom.
Kamar yadda rohoton yazo, a dai daren ranar Asabar ne rikicin ya barke inda aka rushe gidaje 85 bayan an kashe mutane biyar.
Haka a washe garin ranar rikicin ya cigaba a garin Tambora a karamar hukumar Riyom inda mutane sha biyu suka mutu sannan aka rushe wasu gidaje.