Kwamitin Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi na Jahar Kano, Karkashin Jagorancin Shugabar Kwamitin Kuma mai Bawa Gwamna Shawara Akan Harkar Lafiya Dr Fauziyya Buba Idris ta Jagoranci Kaddamar Da Jakadun Yaki Da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi Mata a yankin karamar hukumar Ungogo.
Shugabar Kwamitin Dr Fauziyya Buba wadda Sakatariyar Kwamitin ta jiha Kuma Shugabar kansiloli Mata ta Jihar Kano Hajia Amina Haruna Shanono tayi Jawabi a Madadinta, ta yi Jawabi Mai tsawo game da illar dake tattare da ta’ammali da Miyagun Kwayoyi a tsakanin Mata da Matasa, Inda ta qara cewa Tarbiyar Yara kaso casa’in da Tara cikin Dari na Hannun Iyaye Mata.
Anata Jawabin Wakiliyar Me Dakin Gwamnan Kano Farfesa Hafsat Abdullahi Umar Ganduje, Mai Bawa Gwamna Shawara Akan Kungiyoyi Masu zaman Kansu Kuma Ma’ajin Jam’iyar APC ta Jaha Hajia Yardada Maikano Bichi tayi bayanin yadda Yan Kwamitin a Matakin Karamar Hukuma zasu ka sance.
Ta Kuma yi kira ga Mata a yankin da su tabbata sun karbi Katin zabensu duba da muhimmanci.
Sauran wadanda suka Gabatar da Jawabai a yayin Taron sun hada Kwamishiniyar Harkokin Mata ta Jahar Kano Dr Zahra’u Muhammad Umar, da Shugabar Mata ta Jam’iyar APC ta Jaha Hajia Fatima Abdullahi Dala.
An Dai gudanar da Taron ne a cibiyar Yada addinin Musulunci ta Garin Ungogo, Inda aka bada lambar yabo ga me Dakin Gwamnan Kano Farfesa Hafsat Abdullahi Umar Ganduje, da Shugabar Mata ta Jam’iyar APC ta Jaha Hajia Fatima Abdullahi Dala, da Me Dakin Kwamishinan Kananan Hukumomi Hajia Hafsat Murtala Sule Garo.