Shugaban karamar hukumar Kumbotso ta jihar Kano, Hassan Kauye Farawa, ya kaddamar da wata rundunar tsaro da ta kunshi ‘yan banga da mafarauta har mutum 100 domin tallafa wa jami’an tsaro wajen tabbatar da ingantaccen tsaro a yankin.
Da yake jawabi yayin bikin kaddamar da jami’an tsaro a wani taron masu ruwa da tsaki kan harkokin tsaro a yankin, shugaban ya bayyana cewa majalisa tana tallafawa jami’an tsaro wajen tabbatar tsaron rayuka da dukiyoyi al’umma.
Ya bayyana cewa, domin karfafa gwiwar sarakunan, majalisar ta sanya kowan nen su a kan alawus alawus na Naira 20,000 duk wata daga wannan wata domin kara musu kwarin gwiwa.
Ya kuma bayyana cewa majalisar za ta gina ofishin kwamandojin yankin na jami’an tsaro.
Shugaban karamar hukumar ya kuma sanar da bayar da gudunmuwar sabuwar mota ga sashin ‘yan sanda na Ja’oji da kuma bayar da tallafin babura guda 10 ga wasu zababbun mutanen da za su taimaka wa jami’an tsaro wajen tattara bayanan yaki da miyagun ayyuka a karamar hukumar.
A nasa bamgaren Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, wanda ya sami wakilcin Hakimin Kumbotso, Alhaji Ahmad Ado Bayero, ya umurci dukkan sarakunan yankin da su bayar da gudunmawar da ta dace wajen tabbatar da tsaro mai inganci a yankin.