Jam’iyyar APC na jihar Zamfara, ta kafa kwamitin da zai jagoranci jam’iyyar a jihar a tsakanin kananan hukumomi 14 dake fadin jihar.
Alhaji Liman Liman, shugaban kwamitin jagorancin APC din, shi ne ya kaddamar da kwamitin a yau Litinin a garin Gusau.
Da yake magana a yayin kaddamarwar, Liman ya nemi membobin jam’iyyar da su bai wa marada kunya bisa amanar da aka damka musu wajen ganin sun yi aiki tukuru wajen daidaita jam’iyyar a jihar. Ya nemi dukkanin shugabannin jam’iyyar na kananan hukumomin jihar da su kaddamar da shugabannin jam’iyyar na gundumomin dake karkashinsu.
Liman ya ce jagorancin APC a karkashi Gwamna Mai Mala Buni ya fito da dabaru daban-daban wajen ganin ya karfafa jam’iyyar. Sannan ya jinjinawa tsohon gwamnan jihar, kuma shugaban APC na jihar, Abdul’aziz Yari bisa gudummawar da yake ba su.