Rundunar Sojin sama ta Najeriya ta girke dakaru na musamman domin yaƙar matsalar tsaro a kudancin jihar Kaduna.
Kwamandan rundunar sojin sama da ke Kaduna, Air Vice Marshal Musa Mukhtar ya ce tura dakarun ya biyo bayan umarnin shugaban ƙasa na tabbatar da tsaro da zaman lumana a yankin.
“Dakarun za su ci gaba da zama a kudancin Kaduna matuƙar akwai buƙatar yin hakan, kuma mahukunta za su haɗa ƙarfi da sauran hukumomin tsaro domin magance kashe-kashe da wanzuwar zaman lafiya”, cewarsa.
https://dimokuradiyya.com.ng/yan-bindiga-sun-kashe-mutane-20-a-zangon-kataf-dake-jihar-kaduna/
Ya ce mayaƙan da suka haɗa da sojoji 28 da hafsoshi biyu da kuma likitoci za su ƙara wa takwarorinsu da Hedikwatar tsaro ta tura yankin a kwanakin baya ƙaimi.
Don haka ya buƙace su da su kiyaye hakkokin ɗan Adam da nuna ƙwarewa yayin gudanar da aikinsu.
Ya ƙara da cewa rundunar za ta riƙa kai wa dakarun taimako ƙarƙashin rundunar sojin sama ta Operation Thunder Strike.