Wani ɗan ƙunar baƙin wake ya kai mummunan hari a wani masallaci a birnin Peshawar, a Arewa maso Yamma na ƙasar Pakistan.
Hukumomi sun bayyana cewa harin ya auku ne a ranar Litinin, 30 ga watan Janairun 2023, inda ya halaka aƙalla mutum 20 sannan sama da mutum 96 suka samu raunika. Shafin Linda Ikeji ya rahoto.
KU KARANTA KUMA: Yadda nayi wuff da wata kyakkyawar baturiya cikin kwanaki huɗu kacal -Wani Matashi
Ɗan ƙunar baƙin waken ya tada rigar sa dake ɗauke da bam ɗin ne yayin da sama da mutum 150 suke gudanar da sallah a cikin masallacin.
Tsananin ƙarfin tashin bam ɗin ya sanya rufin masallacin ruftuwa, inda ya raunata mutane da dama, a cewar wani jami’in ɗan sanda Zafar Khan.
Har ya zuwa yanzu dai ba wanda ya ɗauki nauyin kai harin bam ɗin, a cewar wani babban jami’in ɗan sanda Saddique Khan, amma ko a baya an sha ɗora laifin kai irin waɗannan hare-haren akan ƙungiyar Taliban ta Pakistan.
Wani jami’in ɗan sanda mai suna Meena Gul wanda ya samu ya tsira daga harin, ya bayyana cewa yana cikin masallacin lokacin da bam ɗin ya fashe. Yace bai san yadda akayi ya tsira ba tare da wani rauni ba. Yace ya jiyo koke da ƙara bayan fashewar bam ɗin.
Firaministan ƙasar Shahbaz Sharif yayi Allah wadai da harin a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya bayar da umurni kan cewa a tabbatar an ba waɗanda harin ya ritsa da su kulawar da ta dace.
Ya kuma sha alwashin ɗaukar mummunan mataki akan waɗanda ke da hannu a harin.
Wata Matar Aure Ta lakaɗawa Mijinta Dukan Kawo Wuƙa Saboda Yayi Mata Kishiya
A wani labarin na daban kuma, wata matar aure ta lakaɗawa mijinta na jaki bayan ya ƙaro mata kishiya.
Wata mata ƴar shekara 43 a duniya ta shiga hannun hukuma bisa zargin lakaɗawa mijinta dukan tsiya da ƙona gidan da suke zaune a ciki.
Matar mai suna Florence Karakacha ta shiga hannu ne a ranar Asabar, 28 ga watan Janairun 2023, a yankin Navakholio, Kakamega na ƙasar Kenya