By Abbas Yakubu Yaura
Shugaban kasar Cote d’Ivoire Alassane Ouattara ya fada jiya litinin cewa kasashen yammacin Afrika sun kakaba wa kasar Mali takunkumi mai tsauri tare da “mafi girman kai” kan gazawar da shugabannin sojojinta suka yi na maido da mulkin farar hula.
Bayan juyin mulki biyu da aka yi tun shekara ta 2020, sojojin Mali sun yi watsi da alkawarin gudanar da zabe a wata mai zuwa, maimakon haka suka ce za a kai shekaru biyar kafin zaben da zai mayar da kasar ga gwamnatin farar hula.
Dangane da mayar da martani, shugabanin kungiyar hadin kan tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka, sun kakaba takunkumin tattalin arziki da diflomasiyya a ranar 16 ga watan Janairu, a wani mataki da Amurka, EU da Faransa da ta taba yi wa mulkin mallaka suka marawa baya.
Ouattara ya shaidawa manema labarai yayin wata ziyara da ya kai Libreville babban birnin Gabon, inda ya gana da shugaban kasar Ali Bongo Ondimba, “Ba abu ne da za a amince da mulkin soja ya ci gaba da mulki na tsawon shekaru biyar ba, don haka za su iya gudanar da zabe.”
“Mun yi duk abin da ya dace don tabbatar da cewa hukumomin sojan Mali sun shirya zabukan cikin lokaci mai dacewa – tare da rashin jin dadi ne muka sanya wadannan takunkumi.”
Kazalika rufe kan iyakokin kasar da sanya takunkumin cinikayya, shugabannin ECOWAS sun kuma dakatar da tallafin kudi da suke baiwa kasar Mali tare da daskarar da kadarorin kasar a babban bankin kasashen yammacin Afirka.
Tuni dai takunkumin ya fara ci gaba a kasar Mali mai fama da talauci, daya daga cikin kasashe mafi talauci a duniya.
Ouattara ya ce “Halin da jama’a ke ciki na da wahala a Mali da ma kasashe makwabta kamar Senegal da Ivory Coast.” “Muna fatan lamarin zai daidaita da wuri.”
Bayan da gwamnatin Mali ta yi kira da a gudanar da zanga-zangar adawa da takunkumin da kungiyar ECOWAS ta kakaba, dubban mutane ne suka fito kan tituna a Bamako babban birnin kasar ranar Juma’a.AFP
Comments 1