Rundunar ‘yan sanda a jihar Kwara ta tabbatar da cafke babban darektan asibitin Kaiama, Dakta Adio Adebowale, a Edo bayan da ya kashe budurwarsa da wata mata daya a Kwara.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan, Ajayi Okasanmi, ya fitar ranar Lahadin nan a Ilorin.
DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa, Sanarwar ta ce a lokacin da ya karbi mukamin kwamishinan ‘yan sandan jihar Kwara, Paul Odama, yayin da yake bibiyar wasu koke da wasu ‘yan jihar suka rubuta, ya ci karo da wani rahoton wata bacewar wata mace mai suna Nofisat Halidu a karamar hukumar Kaiama ta jihar a ranar 21 ga watan Nuwamban 2021.
“Bisa umarnin kwamishinan, an fara gudanar da bincike kan lamarin kuma ‘yan sanda sun yi aiki a kan wani bayani kan kama wani Dokta Adio Adebowale a Edo,” in ji Mista Okasanmi.
Bayanan da aka samu sun nuna cewa wanda ake zargin bayan kama shi a Edo, ya amsa laifin kashe wata Ifeoluwa, da budurwarsa da aka bayyana ta bata a unguwar Tanke da ke Ilorin a shekarar 2021.
“Binciken ya jagoranci tawagar zuwa babban asibitin Kaiama inda wanda ake zargin ya yi aiki a matsayin babban Daraktan lafiya.
“An tilasta bude ofishin wanda ake zargin kuma an gano gawar wata mace da ba a san ko wacece ba an binne a cikin wani kabari mara zurfi,” in ji kakakin.
Jaridar DailyNigerian ta rawaito cewa, Sanarwar ta kara da cewa, binciken da aka yi a ofishin ya kai ga bude kwandon shara inda daga baya aka gano wata gawar wata mace mai suna Nofisat Halidu da ta bace, wanda mijin, Mista Halidu da sauran jama’ar unguwar suka bayyana ita ce.
A wani labarin kuma: Hukumar NDLEA Ta Kama Kwayar Turamadol Miliyan 13 A Wani Gida
Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta gano kwayoyin Tramadol miliyan 13 a wani katafaren gida da ke unguwar Lekki a jihar Legas.
Femi Babafemi, mai magana da yawun hukumar ta NDLEA ne ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa a shafin sada zumunta a safiyar ranar Litinin din nan.