Kamfanin Dangote a ranar Lahadin da ta gabata ya ce tawagarta da ke sintiri ta kama wani direban ta bisa laifin jigilar katako ba bisa ka’ida ba.
A cewar wata sanarwa da babban jami’in hulda da jama’a na kamfanin, Mista Anthony Chiejina ya rabawa manema labarai, yace an kama direban da babbar motar ne a shiyyar Arewa ta tsakiya tare da mikawa jami’an ‘yan sanda su.
KARANTA WANNAN LABARIN: Tintuni Tinubu Da Arzikinsa Tun Kafin Ya Shiga Siyasa — Dele Alake
Sanarwar ta kara da cewa, “Daga baya an gurfanar da direban a gaban wata kotun majistare da ke Akwanga a jihar Nasarawa bisa laifin zamba cikin aminci inda ya amsa laifinsa kuma aka yanke masa hukuncin daurin watanni hudu a gidan gyaran hali.”
“Yayin da alkalin kotun ya ba da umarnin a saki motar da lodi kayan ga kamfanin da mai shi, ya shawarci kamfanin da ya shigar da kara a kan mai kayan.”
Sanarwar ta kara da cewa, a yankin Kudu-maso-Yamma, tawagar ‘yan sintiri ta lura da wata babbar mota kirar tambarin Dangote, tana ajiye a cikin farfajiyar wani kamfani mai zaman kansa da ke Ode Remo, jihar Ogun, a yayin da take sauke wasu duwatsu.
An ce ‘yan tawagar sun kai rahoton lamarin a ofishin ‘yan sanda na Ode Remo inda suka kama direban da babbar motar.
Sanarwar ta kara da cewa, an gurfanar da direban a gaban kotu.
Sannan Sanarwar ta kara da cewa, “Rundunar ‘yan sintiri na direbobin Dangote sun sake kama wasu direbobin da suka aikata laifin inda suka mika su ga ‘yan sanda da sauran hukumomin da abin ya shafa domin gurfanar da su gaban kuliya.”
“Don haka Hukumar Dangote ta sake sabunta gargadin ga wadanda ke safarar kayan a manyan motocin Dangote ba bisa ka’ida ba, tare da tabbatar da cewa za a kwace irin wadannan kayan da ba a ba su izini ba yayin da direbobi da masu su za su fuskanci cikakken doka.”
Kamfanin ya nemi taimakon jama’a a yakin da ake yi na kawar da kungiyar daga ayyukan jigilar kayayyaki ba bisa ka’ida ba.
Sanarwar ta kara da cewa, “A nan muna sanar da jama’a da su kai rahoton duk wani direban motar Dangote da ke da hannu wajen yin jigilar kayayyaki ba bisa ka’ida ba, an tallafa musu da kwararan hujjoji na irin wannan abu,” in ji sanarwar.
A wani labarin kuma, Ana Fargabar An Kashe ‘Yan sanda, Yayin Da ‘Yan Bindiga Suka Kaiwa Ifeanyi Ubah Hari
An kashe wasu ‘yan sanda da ba a tantance adadinsu ba a unguwar Enugwu-Ukwu da ke karamar hukumar Njikoka a jihar Anambra, yayin da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka kai wa ayarin motocin Sanata Ifeanyi Ubah hari.
Majiyoyi sun ce ‘yan bindigar sun bude wa ayarin motocin wuta, kuma jami’an ‘yan sanda da ke cikin ayarin sun mayar da martani.