Rundunar ‘yan sandan Jihar Filato sun kama wani Albarka Sukuya, fasto bisa zarginsa da yin garkuwa da kansa, Legit.ng ta ruwaito.
Kamar yadda ‘yan sanda suka bayyana, ya tattara kudin fansa ne daga hannun mabiyarnsa bayan yin garkuwa da kansa.
KU KARANTA: Makomar kiristoci na cikin hatsari a 2023, Fasto
Kafin a kama shi, an samu bayani kan yadda ya amshi N400,000 da kuma N200,000 a hannun mambobin nasa.
Dama ba wannan bane karonsa na farko ba. Kamar yadda jami’in hulda da jama’an rundunar, DSP Alfred Alabo ya bayyana, an kama wanda ake zargin ne a watan Nuwamban 2022.
Jaridar Vanguard ta bayyana cewa:
“Rundunar ‘yan sanda ya kama Fasto Albarka Sukuya na Jenta Apata Jos, kan yadda a kai-a kai yake garkuwa da kansa don mambobin cocinsa su tattara masa kudi.
“Ya taba garkuwa da kansa ranar 14 ga watan Nuwamban 2022, da kuma 15 ga wayan Nuwamban 2022, inda ya amshi N400,000 da kuma N200,000, wanda masu tausaya masa suka tattara masa.”
Duk da dai jami’an sun bayyana cewa DPO din ofishin ‘yan sanda na Nasarawa Gwong, CSP Musa Hassan ya gayyaci faston don a fara bincike.
“Da bakinsa ya amsa duk laifukan da ake tuhumarsa da aikatawa.”
Hoton fasto yana bankwana da mambobin cocinsa yayin da yake ka tashi zuwa Aljanna, a cewarsa
Tabbas abubuwan al’ajabi ba sa karewa kuma in har da ranka za ka sha kallo a fadin duniyar nan.
Malaman addinai sun dade suna yin abubuwan bamamaki, wasu su burge jama’a yayin da wasu suke sanya wa mutane tantama.
Akwai abubuwan da suke yi wadanda kan janyo musu mutunci a idon jama’a yayin da wasu ke zubar musu kima da daraja.