By Abbas Yakubu Yaura
An kama wani Insifektan ‘yan sanda, Dele Reuben, bisa zargin tursasa wani direban mota a Legas kan neman takardar izinin saka bakin gilashin mota.
DUBA WANNAN LABARIN: Za’a Iya Yin Oda Akan Sashe Na 84(12) Kada Ya Kawo Rashin Tabbas Na Siyasa
Kamen nasa ci gaba ne ga wani faifan bidiyo na dan sandan yana neman wani direban mota ya ba shi kudi saboda rashin takardar izinin saka bakin gilashin motarsa.
Idan dai za a iya tunawa, Sifeto Janar na ‘yan sanda, Alkali Baba, ya gargadi ‘yan sanda da su daina neman lasisin tuki daga wajen direbobi.
A halin yanzu dai ana tuhumar Insfekta Reuben a sashin provost na hedikwatar rundunar, Ikeja.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin, ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, Abiodun Alabi ne ya bayar da umarnin kama shi.
Hundeyin ya ce an dauki sufeto Dele Reuben a wani faifan bidiyo yana tursasa wani direba don neman izinin shedar saka bakin gikashi da aka dakatar da shi a yanzu.
Ya ci gaba da cewa shugaban ‘yan sandan jihar ya nanata wa jami’ansa da mazajensa ba su da hurumin cin zarafi, karbar na goro da kuma cin zarafin ‘yan kasa.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa a kwanakin baya ne dai hedikwatar ‘yan sanda tayi kira ga yan Najeriya dasu kai rahoton duk wani Ɗan Sanda daya buƙaci a bashi takardar neman izinin sanya Baƙin gilashi na Mota a duk wani wuraren da suke tsayawa a sassan Ƙasar nan.
Mukaddashin jami’in hulda da jama’a na rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ne ya tabbatar da hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi.
Baya ga takardar izinin bakin gilashin, Adejobi ya bayyana cewa ba zai yiwu ba ga kowane dan sanda ya nemi takardar izinin kwastam ko wasu takardun da ba su dace da aikinsu ba.