An kama Jami’in Kula da Gidan Yari kan ɓatan bindigogi, Alburusai
Kwanturola Hukumar Kula da Gidajen Yari na jihar Kogi, David Igbago, ya bayar da umarnin cafke wani jami’in Hukumar nan take bisa laifin bacewar bindigogi biyu da wasu alburusai na Hukumar.
KARANTA WANNAN LABARIN: CBN ta bada lasisin gudanar da Harkoki ga TajBank a faɗin Najeriya
Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na Hukumar Gidan Yarin jihar, DCS Nihi Sesan, wanda aka rabawa Manema Labarai a Abuja ranar Laraba, bai ambaci sunan wanda ake zargin ba.
Sai dai ta ce an sanya jami’in ne a tsarin Shuwagabanci kafin a miƙa shi ga Hukumar tsaro da ta dace domin ci gaba da yi masa bincike.
Sanarwar ta ce an gano abubuwan da suka ɓace ne a yayin gudanar da binciken makamai da alburusai da aka saba yi duk wata a cikin rumbun ajiyar makamai na Hukumar.
Igbago ya sha alwashin tabbatar da cewa ba a bar wani abu ba wajen bankado al’amuran da suka dabaibaye wannan aika-aika tare da gurfanar da masu laifi a gaban kuliya.
Ya kuma bai wa jama’a tabbacin da ya ke da shi na tabbatar da tsaro a jihar Kogi baki daya da ma cibiyoyin kula da lafiya a jihar.