Hukumar hana safarar mutane (NAPTIP) ta kama wani Kwamandan Hisbah da Mai Unguwar Fagge a jihar Kano, bisa zargin sayar da jariri ɗan shekara ɗaya a Jihar Imo.
Shugaban NAPTIP reshen Kano, Shehu Umar a hirarsa da ‘yan jarida, inda ya ce waɗanda ake zargin sun sayar da jaririn da wadda ta siye shi sun amsa tambayoyin hukumar.
Wata majiya ta ce an bai wa jami’an Hisban alhakin kula da jaririn ne sakamakon jefar da shi da iyayensa suka kayi a kano.
An ce Kwamandan na Hisbah ya yi amfani da damar da haɗin kan Mai unguwar suka sayar da jaririn.
Shugaban na NAPTIP ya ce an ƙwato yaron da ake zargin masu laifin sun sayar ne daga wajen mahaifiyar matar wadda suka kamo daga jihar Imo.
“Bayan samun rahoto kan lamarin, mun gudanar da binciken da ya taimaka muka kamo mahaifiyar Loveth a jihar Imo,” inji Umar.
Ya ce an bayar da belin waɗanda ake zargin amma akwai yiwuwar su kwashe shekara biyar a gidan kaso ko tarar naira miliyan biyar in har zargin ya tabbata.