Wani mayaudarin Likita mai suna Obiako Chukwuemeka da ya bayyana cewa shi likita ne da ke aiki da Majalisar Dinkin Duniya a matsayin mai bayar da agajin jin kai a Asibitin kasa da ke Abuja, ya shiga hannun hukuma.
Bayan da bincike ya tabbatar da cewa likitan na Bogi ne tuni aka mika shi hannun jami’an tsaron yan sanda a Abuja.
Wata majiya mai tushe a rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya ta tabbatar da cewa, Chukwuemeka wanda har yanzu ba a san asalinsa da shekarun sa ba, ana tsare da shi har sai an gurfanar da shi a gaban kuliya.
KARANTA ANAN: Katsina: Yan Bindiga Sun Kama Wani Barawo Tare Da Mikashi Ga Hukuma
Majiyar ta ce, “Asibitin kasa da ke Abuja, ya mika wani likitan jabu, Obiako Chukwuemeka wanda ya yi kama da wani likitan Majalisar Dinkin Duniya kan ayyukan jin kai ga ‘yan sanda a ofishin ‘yan sanda na Birnin tarayyar.
“Yanzu haka yana hannunmu, kuma nan ba da jimawa ba za a gurfanar da shi gaban kotu.”
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa wannan dai na zuwa ne kimanin mako guda bayan da Ministan babban birnin tarayya, Muhammad Bello, ya zargi maziyartan jihohin da ke makwabtaka da su, ‘yan kasuwa, da mabarata da hannu wajen tabarbarewar tsaro a Abuja.
Ya kara da cewa gwamnatinsa zata ci gaba da sanya ido, tare da gurfanar da duk wani bata gari a gaban kuliya don girbar duk abinda ya shuka.
A wani labarin kuma: Ƴan Ta’adda sun tare hanyar Kaduna, sun kashe mutum 2, sun sace wasu
Wasu Ƴan ta’adda sun tare hanyar Birnin-Gwari zuwa Funtua a karamar hukumar Birnin-Gwari a jihar Kaduna, inda suka kashe mutane biyu tare da yin awon gaba da wasu da dama.
Shugaban kungiyar masu ci gaban masarautar Birnin-Gwari (BEPU), Ishaq Kasai, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, ya ce ‘yan ta’addan sun kashe wani Direba tare da sace matafiya da dama.