An kama masu haƙar Ma’adinai 12 ba bisa ka’ida ba a Ogun
Jami’an hukumar tsaro ta So-Safe Corps mallakin jihar Ogun sun kama wasu masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba 12 a yankin Ogun ta Gabas.
DAILY POST ta samu labarin cewa an kama mutanen 12 a tsakanin ranakun 28 zuwa 30 ga watan Satumba, “a lokacin da suke satar dukiyar gwamnatin jihar.”
KARANTA WANNAN LABARIN: Sanata Uba Sani Ya Yaba Da Wani Taron Horaswa Ga Malaman Addinin Musulunci
Kakakin Rundunar So-Safe, Moruf Yusuf, ya shaida wa wakilinmu cewa, an tsare masu hakar ma’adinan ba bisa ka’ida ba ne a kauyen Abeku Adekanmbi da ke karamar hukumar Ijebu ta Arewa a jihar Ogun.
Yusuf ya bayyana cewa an kama mutanen 12 “a lokacin da suke satar albarkatun ma’adinai kamar gawayi da zinare a karkashin kasa.”
A cewarsa, Kwamandan So-Safe, Soji Ganzallo, ba tare da bata lokaci ba, ya ba da umarnin a mika rahoton binciken farko na wadanda ake zargin zuwa hedikwatar hukumar ta jihar da ke Abeokuta.
Ganzallo ya kuma bayar da umarnin a gurfanar da sauran masu laifin da suka tsere ta hanyar babura.
Tuni dai aka mika wadanda ake zargin zuwa hedikwatar ‘yan sanda ta Ijebu Igbo domin ci gaba da bincike tare da gurfanar da su gaban kuliya, in ji Yusuf.
A wani labarin kuma: Ƙwararru sun koka rashin zuba kuɗaɗe ga Bincike a ɓangaren lafiya a Najeriya
Kwararru sun ce rashin zuba kudade a ɓangaren lafiya na kawo cikas ga bincike a Najeriya.
Sun bayyana hakan ne jiya a Abuja a yayin taron shekara na 6 na kungiyar NISA da aka yi mai taken ‘Dorewar Shirye-shiryen Aiwatarwa & Bincike’.