Wani matashi a Najeriya ya janyo dauki hankalin jama’a yayin da ya fara zuwa aiki a sabon ofishin da aka dauke shi aikin.
Matashin wanda ba a ambaci sunansa ba, ya yi wani abin tir da Allah wadai ne bayan da aka kama shi yana satar waya a ofishin.
Ko da yake matashin ya musanta zarginsa da ake yi bayan da aka tunkareshi da maganar ɓacewar wayar, to amma na’urar sirri ta CCTV ta bayyana ƙarara yadda yake wannan aika-aika.
Wani Matashi mai suna Opayemi Babalola da ya wallafa wannan lamari a shafinsa na Instagram, ya ce daga bisani dai matashin ya amsa laifin sa tare da bada haƙurin cewa hakan ba zai sake faruwa ba.