Rundunar ‘yan sandan farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen jihar Kwara, ta tabbatar da cafke wasu mutane hudu da ake zargi da aikata laifuka a wani samame da ta kai a unguwar Rore da ke wajen Omu Aran a karamar hukumar Ifelodun ta jihar.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar NSCDC a jihar Kwara, Babawale Zaid Afolabi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.
A cewarsa, wadanda ake zargin sun hada da Olanrewaju Adesoye Mai shekara (24), Isaac Abraham (28), Tope Fadeyi (33) da Abdulateef Wasiu, (23). Inda Kuma ya ce har yanzu wasu ‘yan kungiyar guda biyu ana Neman su ruwa a jallo.
“Jami’an NSCDC da ke Omu Aran, da suke gudanar da bincike, sun tarwatsa maboyar wasu miyagu da suka addabi yankin a ‘yan kwanakin nan.
“A lokacin da aka kama su, an kwato bindigogi biyu na gida, harsashi guda biyar, fakitin kwayar tramadol, laya na gida, Wiwi da kuma wayoyin hannu guda shida daga maboyarsu.” Babawale ya ruwaito