Jami’an tsaro a Birtaniya sun yi ram da wasu mutane takwas bisa zarginsu da cun zarafin dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Tottenham dake ƙasar Ingila Son Heung-min.
Da ma kuma tun da farko kimanin makonni biyu kenan da suka gabata ake tsare da wasu mutane hudu a ofishin yan sanda suna amsa tambayoyi mai tsada bayan wasan da Tottenham ta sha kashi hannun Manchester United 3:1.
“An chafke mutanen ne bisa amfana da muggana kalamai da wallafa rubutun iska dake nuna kiyayya ga dan wasan” Cewar Yan sandan birnin Landan.
Da ma dai tun ana tsaka da kece rainin Manchester United da Tottenham din ne aka fara mishi munanan kalamai bayan da ya ci kwallo sannan aka kashe.
Su sai wadannan mutane takwas an chafke su ne a wurare daban-daban da suka hada da Ingila da kuma Wales.