• Rundunar Yan sandan jihar Kano ta kama Mutane 5 da zargin yin Luwadi a Kano.
• Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar ta Kano ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce ankama su ne a ranar 16 ga watan Yulin Shekarar 2021.
• Ya Kara da cewa za’a gurfanar dasu agaban Kotu da zaran ankammala gudanar da bincike.
Rundunar yan sandan jihar Kano ta tabbatar da kama mutune biyar da ta ke zargi wurin yi wa wani matashin Dan shekara 20 Mai suna Tajudden Hashim luwadi.
Mai Magana da yawun rundunar yan sanda jihar DSP Abdullahi Haruna ne ya bayyana hakan, a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a yau juma’a a garin kano.
Mai Magana da yawun rundunar ya bayyana cewa, an kama wadanda ake zargin ne a ranar 16 ga watan Yulin 2021 a garin Mandawari, dake karamar hukumar Gwale, inda ya ce, an sami nasarar kama wadanda ake zargin ne, bisa korafe korafen da al’umar yankin su ka shigar.
Lokacin da ake tambayan Hashim wanda lamarin ya faru dashi ya ce, mutanan da su ka yi mishi wannan aika-aikan sun hada da Ahmed Inuwa Mai shekara 34, da Nasiru Isyaku Mohammed Mai shekara 48, Lawal Uba Mai shekara 31, Auwalu Uba Mai shekara 40 da kuma Rabi’u Shari Mai shekara 33, inda ya ce, sun ai wani wuri ne su kayi luwani da shi daya bayan daya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ambaliyar ruwa ya lalata kaddarorin Naira Milliyan 60 a Kano
Ya ce bayan wani lokaci sai ya fara fama da ciwon ciki mai tsanani
Daga bisani an kai Hashim asibitin Muhammad Abdullahi Wase dake cikin garin Kano, inda anan ne aka kula da lafiyar shi, daga bisani kuma aka kama wadanda ake zargi.
A cewar DSP Abdullahi ya ce, dukkannin wadanda ake zargin sun amsa laifin su kuma za’a gurfanar da su a gaban Kotu, da zaran an kammala gudanar da bincike.