An kama Tsoho mai shekaru 68 da ya yi lalata da ƙaramar yarinya a Osun
An gurfanar da wani mutum mai shekaru 68, Ayodele Faremi, a gidan yari bisa zarginsa da lalata da wata yarinya ‘yar shekara 10 a Osogbo, babban birnin jihar Osun.
An kama Faremi ne a ranar Lahadi bayan da aka kai karar ofishin ‘yan sanda na Dada Estate, Osogbo.
KARANTA WANNAN LABARIN: PDP ta caccaki Gwamnatin jihar Kwara na shirin kama mambobinta
DAILY POST ta tattaro cewa wata Folashade Ashafa ta bayyana cewa yaron ‘yar uwarta (an sakaya sunansa) an yi mata kazanta ne a lokacin tana ‘yar shekara tara da Faremi.
Sanarwar ta kara da cewa wanda ake zargin ya kuma ci gaba da kwanta wa da’ita sau biyu a cikin watan Mayu da kuma sau daya a watan Agusta 2022.
An kuma bayyana cewa mutumin mai shekaru 68 a duniya yakan baiwa yara masu kasa da shekaru wani magani na musamman su sha a duk lokacin da ya gama aikata rashin da’a.
A halin da ake ciki, an gurfanar da Faremi a gaban kotun majistare a ranar Litinin da laifuka uku.
Laifin da ake zargin an aikata yana da hukunci a karkashin sashe na 31(1)(2) da 32 da 360 na dokar kare hakkin yara na jihar Osun 2007.
Alkalin kotun, O.A Daramola ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake zargin a gidan yari tare da dage sauraron karar zuwa ranar 25 ga watan Oktoba.
A wani labarin kuma: Yajin aikin ASUU: Dalibi ya maka Malamai, Gwamnatin Najeriya, jihohi 36, da Majalisa a Kotu
Wani dalibin jami’a, Soohemba Aker, ya roki wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, da ta bayar da umarnin dakatar da ayyukan hukumar tattara kudaden shiga da rabon kudi da kasafin kudi (RMAFC) har sai an warware yajin aikin ASUU.
Shi ma dalibin shekarar karshe a fannin shari’a a Jami’ar Jihar Benue, ya kuma nemi umarnin dakatar da aiki na Kwamitin rarraba kuɗaɗe na Tarayya (FAAC).