Hukumar NDLEA ta kama wani tsohon dan wasan kwallon kafa Emmanuel Okafor a filin jirgin saman Murtala Muhammed dake Ikeja bisa laifin safarar hodar iblis.
Kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi ne ya bayyana hakan, a ranar Lahadi a Abuja cewa an kama Mista Okafor ne a lokacin da ya taso daga Sao Paulo, na kasar Brazil ya biyo ta Addis Ababa.
KARANTA ANAN: Manoma Sama da 50 Ne Suka Hallaka A Jihar Taraba
Mista Babafemi ya bayyana cewa wanda ake zargin yana dauke da hodar iblis mai nauyin kilogiram 1.4 da aka boye a hannun jakunkunansa da kuma a saman jakunkunan.
Ya kara da cewa an kama matashin mai shekaru 33 dan asalin karamar hukumar Arochukwu da ke jihar Abia ne a ranar 26 ga watan Satumba bayan jami’an yaki da muggan kwayoyi sun bankado inda ya boye kwayar.
Ya kara da cewa, an kuma kama wani dan kasar Brazil mai suna Chinedu Ibeh a ranar 26 ga watan Satumba da ya isa filin jirgin saman Legas daga Sao Paulo na Brazil, shi ma ta hanyar amfani da jirgin Ethiopian Airlines.
Ya kuma bayyana cewa Mista Ibeh ya fito ne daga Ahiazu a karamar hukumar Mbaise ta jihar Imo kuma an same shi boye da 3.2kg na Black Cocaine wanda aka fi sani da “Lucci’ a cikin karyar jakunkunansa guda biyu.
Femi ya ce da zarar sun kammala bincike zasu mika shi gaba, domin fuskantar hukunci daidai da laifin da ya aikata.
A wani labarin kuma: Ba Zan Kara Biyan Duk Wani Malamin Dake Yajin Aikin ASUU Ko Si-Sin Kwabo Ba—Gwamna Tambuwal
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto ya dakatar da biyan albashin malaman jami’ar da ke yajin aiki.
Kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta fara yajin aikin a watan Fabrairu saboda bukatar inganta walwala da sauran su.