• Rundunar Yan sandan jihar Filato ta kama wadanda su kayi garkuwa da Mahaifin Tsohon Gwamnan Filato.
• Wanda ake zargi da kitsa karkuwa da Mahaifin Tsohon Gwamnan su takwas aka kama a maboyar su.
• Wannan dai bashine karo na farko da ba daka yi garkuwa da Mahaifin Tsohon Gwamnan.
Kungun Mutum takwas na wadanda su kayi garkuwa da Mahaifin Tsohon Gwamnan jihar Filato Jushua Chibi Dariye sun shiga hannu, a karamar hukumar Bokkos dake jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wata sabuwa: Kamfanin Airtel bai sabunta Lasisin shi ba inji NCC
Jami’in Hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar Uba Gabriel ne, ya tabbatar da nasarar kama masu Garkuwa da mutanan, inda ya ce, jami’an hadaka da na yan sanda ne, su kayi nasarar kama wadanda ake zargin a maboyar su.
Idan za’a iya tunawa dai, an yi garkuwa da Chibe Dariye ne a watan Yunin shekarar 2020 a kauyen shi na Mushere, dake cikin karamar hukumar Bokkos, inda ya ba a sakejin labarin shi ba, sai a makon jiya da aka kama wadanda ake zargi, da kitsa garkuwa da shi.
Jaridar Daily Trust ta ruwai to cewa, wannan na iya kasance wa karo na biyu, da aka yi yunkurin garkuwa da Thibi Dariye a kauyen shi na Mushere.
Inda aka taba garkuwa da shi, a cikin shekarar 2015, amma daga bisani aka sake shi, bayan an biya wasu makudan kudade a matsayin kudin fansa, ga masu Garkuwa da mutane.
A wani Mai kama da haka kuma
Yan bindiga sun kashe jami’an yan sanda 13 da kuma wasu Mutum uku, a wani hari da yan bindiga suka kai a yankin Kurar Mota, dake karamar hukumar Bundugu na jihar Zamfara.
A cewar mazauna yankin sun ce, yan bindigan sunyi yunkurin farmakan yankin Magami ne, dake da nisan kilomita 50 gada Kudancin Gusau babban birnin jihar, sai jami’an soji suka dakile yunkirin nasu.
” Sun janye yunkurin su ne, bayan jami’an soji sun dakile yunkirin na su, daga nan ne suka nufi wani yanki dake kan hanyar Magami-Dankurmi zuwa Dangulbi inda a nan ne, su ka kashe Mutum guda da kuma fasa shaguna hudu” inji wani mazaunin garin.
“Bayan nan kuma su ka farmaki yankin Kurar Mota, inda suka kai wa jami’an yan sanda dake kusa da wani dakin Shan Magani hari, daga bisani kuma su ka famtsama cikin daji.” Inji shi.
“Jami’an da aka kashe da kuma wadanda suka sami raunuka an kai su cikin garin Gusau a Motocin rundunar yan sanda, kuma nan ne naga gawar-wakin goma sha uku na jami’an yan sanda, sai dai gada bisani, na ga Motocin jami’an yan sanda dama sun nufi inda lamarin ya afku.” Inji shi
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar ta Zamfara SP Muhammad Shehu, ya yi alkawarin yi wa wakilin mu karin bayani da zaran ya kammala tattara bayanai, kan rahoton kai harin.