Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta yi nasarar cafke wani mutum mai suna Abba Musa mazaunin unguwar rijiyar zaki a jihar, dauke da kwayar Tramadol wadda darajarta ta kai naira miliyan 25.
Yan sandan sun kama Abba Musa ne dan kima I’m shekaru 30, dauke da fakitin Tramadol guda 500, da aka koda su a cikin motar da yake tunawa, akan titin Ahmadu Bello way, a ranar 31 ga watan Yuni da misalin karfe 10:30 na dare.
Jami’an Yan sandan caji ofis din Badawa ne suka yi nasarar kama matashin, wanda kuma bayan sun kama shi ya ce motar Ba yasa bace, don shima aikensa akayi da ita don da ya kaiwa wani a Yan Kaba.
KARANTA KARIN WANNAN LABARIN: Yan Kannywood sun shirya kalubalantar matakin IGP na kasa a kotu kan furucinsa gare su
Ƙwayar dai a bincike yan sandan sun gano cewa an shigo da ita Kano ne, daga Onitsha dake jihar Anambra.
Binciken da rundunar ta gudanar ya nuna cewa wanda ake zargin ya bayyana cewa motar mallakin wani abokin sa ne mai suna Sulaiman Danwawu mazaunin unguwar Rijiyar Zaki ce.
A cewar sanarwa da kakakin rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar rundunar ta yi nasarar kama mai motar, inda ya tabbatar da cewa ya tawo da kwayar ne daga Anambra domin siyar da ita a jihar Kano.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa tuni dai mataimakin Kwamishinan ‘yan Sanda DCP Abubakar Zubairu ya bada umarnin ci gaba da bincikar lamarin.