…Wani mutum dan shekara 48, Adekola Adeshina, ya shiga hannun jami’an ‘yan sanda a Abuja bisa zargin lalata da ‘yar makwabcinsa ‘yar shekara goma. Kwamishinan FCT na.
Wani mutum dan shekara 48, Adekola Adeshina, ya shiga hannun jami’an ‘yan sanda a Abuja bisa zargin lalata da ‘yar makwabcinsa ‘yar shekara goma.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Kwamishinan ‘yan sanda na babban birnin tarayya Abuja, CP, Sadiq Abubakar, wanda ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da wanda ake zargin a shedikwatar rundunar, ya ce an kama wanda ake zargin ne biyo bayan korafin da wata Rose Solomon da ke zaune a bayan gidan Prince & Princess Estate, a Abuja.
KARANTA HAKANAN Buhari Ya Nuna Rashin Amincewarsa Da Cin Zarafi Da Lalata A Jami’o’i
Ya bayyana cewa bayan da aka yi masa tambayoyi wanda ake zargin ya amsa a rubuce cewa ya aikata laifin da dama.
Ya ci gaba da cewa, “Yayin da yarinyar ‘yar shekara 10 ke duba lafiyarta, muna kira ga iyaye da masu kula da su da su kula sosai kan sauye-sauyen dabi’un da ake samu a unguwannin su, tare da tabbatar da cewa an samar da matakan da za a bi wajen ganin an magance matsalar don kare su daga aikata laifukan jima’i.”
CP ya umurci jama’a da su ci gaba da yin taka tsantsan da yin kira da koke-koke ta layukan gaggawa kamar haka: 08032003913, 08061581938, 07057337653 da 08028940883. Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito
A Wani Labarin Kuma Masarautar Bichi Ta Kaddamar Da Tashar Wutar Lantarki Ta Sola A Kauyen Yal’Iami
Mai martaba Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero ya kaddamar da sabuwar tashar samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana a kauyen Yal’lami dake karamar hukumar Bichi ta jihar Kano wanda masarautar ta bayar tare da hadin gwiwar wani kamfani mai suna Sand Stream Nigeria Limited.
Yayin da yake kaddamar da tashar, Sarkin ya ce, “aikin wani bangare ne na kokarin da Masarautar ke yi na samar da yanayi mai kyau ga al’ummar yankin da kuma makwabta”.