Rundunar yan sandan jihar Imo, ta tabbatar da kamen wasu daga cikin jami’an ta, wadanda suka tursasawa wani matafiyi karɓar kuɗinsa Naira 60,000.
Rundunar ta sanar da hakan ne cikin wata sanarwa, da ta rabata ga manema labarai a yammacin Laraba, tare da bayyana sunan Victor Agunwah a matsayin wanda lamarin ya faru akansa.
To sai dai sanarwar Bata bayyana sunayen jami’anta wadanda suka aikata wannan aika-aika ba, amma dai ta ce zasu fuskanci hukunci dai dai da laifin da suka aikata.
Tun a baya dai Victor Wanda aka kwaci kudin a wajensa, ya shigar da Korafinsa ga kwamishinan yan sanda na jihar Rabiu Hussaini, domin korafin kwace masa kudi da jami’an suka yi ta hanyar amfani da na’urar cirar kudi ta POS.
Kuka kafin su karbi kudin sai da suka ci mutuncin sauran fasinjojin dake cikin motar, sannan daga bisani suka karbi kudin a wajen mutumin.
Sanarwar ta ce tuni kwamishinan yan sanda ya sa aka kamo jami’an kuma yanzu haka suna tsare a shelkwatar hukumar, domin cigaba da bincike.