By Ishaq Dabai
Kwanaki kadan bayan kama wani dan sanda mai ritaya da wani mutum daya da Sinƙin ganyen hemp 320, Wanda Kuma kuɗin wanan ganyen zai kai Naira miliyan 9.5. Rundunar Operation SAFE HAVEN, ta sake cafke wani dauke da miyagun kwayoyin mai yawa, wanda ake zargi ciki har da wiwi, wanda kudin su ya kai Naira miliyan 7.5.
Kamar dai yadda lamarin ya faru a baya, ana zargin an boye sinadarin a cikin motar Toyota Camry mai lamba Lagos, KJA 150 EG. Inda kuma an cafke wadanda ake zargin a yayin aikin bincike a kan hanyar Manchok zuwa Jos dake karamar hukumar Kaura ta jihar Kaduna.
Dangane da sabon lamarin, jami’in yada labarai na soji, Manjo Ishaku Takwa a cikin wata sanarwa da ya fitar a Jos, ya ce “Sojojin karkashin rundunar Operation SAFE HAVEN, a ranar Talata, 14 ga Satumba 2021 sun tarwatsa wani rukunin miyagun kwayoyi tare da gano sinƙin kwayoyin 248.
Wadanda ake zargin sun yi iƙirarin cewa an ba su kwangilar isar da haramtattun kayan zuwa Yola, na jihar Adamawa daga jihar Ondo.