Akala mutane miliyan 7 da dubu 400 ne ake sa ran za su kada kuri’ar su a zaben shugaban kasa da na ‘yan Majalisu da zai gudana a gobe Lahadi a Jamhuriyar Nijar.
Zaben da zai zama irinsa na farko da za a mika mulki daga farar hula zuwa farar hula bisa turbar Dimokradiyya a tarihin kasar, duk da barazanar tattalin arziki da kuma hare-haren ‘yan ta’adda.
A cikin makon da ya gabata ne ‘yan takara 7 daga cikin 30 dake neman maye gurbin shugaban kasa Issofou Mahammadou suka shigar da kara kotu inda suke bukatar ganin ta haramtawa Bazoum takara, amma kuma kotun tayi watsi da bukatar su.
Daga cikin wadannan’ yan takara akwai tsohon shugaban mulkin soji Janar Salou Djibo da Amadou Boubacar Cisse da Ibrahim Yacouba da Omar Hamidou Tchiana.
Sauran sun hada da Hamissou Mahaman Moumouni da Mamadou Moustapha Mamadou da Aboulkadri Alpha Oumarou da kuma Djibrilla Bare.
Dan takara bangaren gwamnmati Bazoum Mohammed a wata zantawa da AFP ya dau alkawarin dawo da ilahirin ‘yan gudun hijira na gabacin kasar gidajen su nan da karshen shekara ta 2021.
A bangaren yan adawa, dawo da tsaro,bunkasa ayukan noma na daga cikin manyan ayuka da suke sa ran dawo da su a wasu yankunan da rashin tsaro ya tilastawa mazauna yankunan kauracewa gidajen su.