Zamfara ta karbo mahaifin yar makarantar jangebe da wasu mutun 9 ta hanyar sulhu
Wakilinmu Shuaibu Ibrahim Gusau
Gwamnatin jihar Zamfara, karkashin jagorancin, Hon Bello Muhammad Matawalle, ya samun nasarar amso mahaifin daliban nan da tace taga mahaifinta, tare da wasu mutun tara da aka sace ba tare da kudin fansa ba.
A jiya ne aka kawo wadannan mutanen a gidan gwamnatin jihar Zamfara, ciki harda mata da yara, wadanda aka sace sun kwashe sama da watanni uku ana garkuwa da su.
Sun bayyana cewa an sace su ne a garin Gwaram da ke karamar hukumar Talata Mafara ta jihar cikin wani daji da ake kira da suna Kare kukanka a karamar hukumar Maru.
Gwamna Bello Muhammad Matawalle wanda kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida Abubakar Dauran ya wakilta, ya ce an kubutar da su ba tare da kudin fansa ba, an yi amfani ne ta hanyar shirin zaman lafiya da gwamnatin Matawalle ke yi a yanzu.
Gwamnan ya yi alkawarin ci gaba da tattaunawar zaman lafiyar, kamar yadda ya ce domin hanya ce da za ta samar da dauwamammen zaman lafiya a Jihar Zamfara dama kasa baki daya.