Gwamnan Jahar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje a ranar Alhamis 5 ga watan Ogustan Shekarar 2021, ya gabatar da takarda a matsayin shi na Babban Bako, a taron da Kungiyar Yan Jarida na Jami’iyyar APC wato-APC Press Corps ta shirya kashi na 2 na wata uku-uku, mai taken “Dorewar Hadin Kan Nigeria ba tare da rabuwa ba: Kamar yadda yake a yanzu”, Wanda ya gudana a Dakin taro na Ladi Kwali, dake otel na Sheraton a Abuja.
Takardar ta tattauna muhimman batutuwa da dama masu Mahimmanci, musamman ta bangaren taken da aka sanyawa taron, Wanda ya lura dacewa, Sanatoci da suka hada da Rochas Okorocha, Barau I. Jibrin da sauran manya, da suka kasance Karkashin jagorancin Mrs Eugenia Abu, ta bayyana irin muhimmiyar rawa da masu bayanin suka yi.
A lokacin taron, manyan baki da suka halarta, sun hada da Gwamnan Jahar Yobe, Kuma Shugaban Kwamitin Ruko na Jami’iyyar APC Mai Mala Buni, Wanda ya samu Wakilcin tsohon Shugaban Majalisar Dattijai Mr Ken Nnamani, da Mambobin Majalisar Dokoki ta Kasa da Sauran su.
KARANTA WANNA LABARIN: Rage Albashin ma aikata ba na dun dun dun bane, inji Gwamnatin Yobe
An baiwa Gwamna Ganduje lambar yabo domin nuna yabawa akan irin salon Mulkin sa daga Kungiyar Yan Jarida na Jami’iyyar APC wato-APC Press Corps, Wanda hakan ya nuna irin dimbin tsare-tsare da shirye-shiryen ayyukan cigaba da Gwamnan yayi.
Tsohon Shugaban Majalisar Dattijai ta Kasa Ken Nnamani ya mika lambar yabon ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
Gwamnan ya samu rakiyar Kwamishinan Yada Labaru Kwamared Muhammad Garba, da Dan Majalisa Mai Wakiltar Karamar Hukumar Bichi Injiniya Abubakar Kabir Bichi, da sauran Manyan Jami’an Gwamnati.