Akalla mutane 210 suka rasa rayukan su a Yammacin kasar Habasha, a makon da ya gabata, biyo bayan hare-hare da masu fafutukar neman ballewar daga Kasar wato Oromo Liberation Army suka Kai wa cibiyoyin farar hula a yankin.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ne ya bayyana hakan, inda Kuma ya bayyana cewa, tuni Gwamnatin kasar ta kafa Hukumar Kare Hakkin Dan Adam domin Kai wa fararan hula dauki.
Kazalika Hukumar ta ce, wata kungiyar yan awaren ta kai hari kan mazauna gundumar Gida Kiremu, da ke yammacin Yankin Oromia a ranar 18 ga watan Agustan shekarar nan, inda ta kashe mutane 150.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wani Jirgin Sama ya Kai wa Fasinjojin jirgin ruwa hari a Rivers
Washegarin ranar ma, mayakan sun kaddamar da sabon farmaki a yankin, inda suka kashe wasu mutane 60.
har’ilayau hukumomin kasar sun bayyana wadandan hare -haren a matsayin na kabilanci.
Tun da farko, Kamfanin dillancin labarai na Reuters, ta ba da rahoton asarar rayuka sama da 150 a ranar farko da aka kai harin, in ji TASS.
Comments 1