Daga Abdullahi Kebbi
Fulani 15 ne suka rasa rayukansu sakamakon wani Hari da aka kai musu, cikin wata sanarwa da Sakatare Janar Na kungiyar Miyetta Allah Muhammad Mainasa ya fitar ya bayyana cewa an kashe fulani goma sha biyar a wani hari da aka kai musu a jahar Kogi.
A wani bangare kuma gwamnan jahar kogi ya fitar da wata sanarwa inda yace idan jami’an Gwamnati da Sarakunan da ke yankin basu Bayyana Maharan nan ba nan da kwanaki 7 to za’a sauke su daga mukamansu.
Sai dai Gwamnan ya bayyana cewa an aika da jami’an tsaro yankin da lamarin ya faru.
Gwamnan yaci gaba da cewa bazan iya siyasa da wasa da rayukan al’umma ba, sabida haka ina gargadin masu haifarda sabon rikici saboda siyasa cewa, su shiga taitayin su.