Asusun Bunkasa Ilimin Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bayyana cewa, an kashe malaman makarantun boko dubu 2 da 295 a yankin arewa maso gabashin Najeriya a cikin shekaru 11 da aka kwashe ana fama da rikici a yankin.
An dai yi wa Malaman kisan gilla ne tsakanin 2009 zuwa 2020.
Shugabar Ofishin Asusun mai kula da shiyar jihar Borno ta Najeriya, Phuong Nguyen ta bayyana haka a wata hira ta musamman da jaridar Premium Times albarkacin zagayowar ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin nazari game da kare bangaren ilimi daga fuskantar hare-hare a sasaan duniya.
Kwararriyar Jami’ar wadda ta yi aiki a wasu kasashen duniya da suka yi fama da tashe-tashen hankula ta ce, hare-haren ta’addanci sun yi zagon-kasa ga fannin ilimi a yankin arewa maso gabashin Najeriya, yayin da aka lalata makarantu dubu 1 da 400, sannan kuma aka tilasta wa sama da yara miliyan 1 kaurace wa azuzuwansu.
Wannan matsalar ta ta’addanci ta tilasta wa hukumomi rufe makarantun boko daga watan Disamban 2013 zuwa watan Yunin 2015 a jihar Borno, yayin da a Yobe da Adamawa, aka rufe makarantun na wani kankanin lokaci.
Jami’ar ta UNICEF ta ce, hare-haren makamai da rikcin kabilanci da bala’o’i da kuma tabarbarewar tattalin arziki duk sun dada fadada gibin da ake da shi a Borno da Adamawa da Yobe dangane da ilmantar da yara kanana.
Alkaluma sun nuna cewa, kashi 52 cikin 100 na yaran da ke tsakankanin shekarun shiga makaranta a matakin farko, ba su taba halartar makarantar ba a yankin arewa maso gabashin Najeriya, adadin da aka bayyana a matsayin mafi girma a Najeriya, idan aka kwatanta da sauran yankunan kasar.
Rikcin Boko Haram ya tilasta wa miliyoyin mutane kaurace wa muhallansu, lamarin da ya sa aka sama musu matsuguni na wucean-gadi a sansanonin ‘yan gudun hijira.
Matalsar ta gudun hijira ta haifar da cikas ga kananan yara musamman ma ga ‘ya mace wajen neman ilimi, la’akari da nauyin da ya karu a kanta na kula da iyalanta da kuma aikace-aikacen gida.