Kimanin mayakan ISWAP 25 da ke tserewa hare-haren sama na sojojin Najeriya sun nutse a cikin kogin Chadi da ke kusa da yankin Marte na tafkin Chadi, Wanda sansanin ‘yan ta’adda ne a jihar Borno da ke Arewa maso Gabas.
Kamfanin dillancin labaran PRNigeria ya bayar da rahoton cewa, jiragen yakin soji da suka hada da Super Tucano na rundunar sojojin saman Najeriya sun kai farmaki kan sansanonin ‘yan ta’addar Daesh a yammacin Afrika a tsawon mako guda da wani harin sama da aka kai wanda ya yi sanadin mutuwar ‘yan ta’adda da dama.
Wani jami’in leken asiri da ke zaune a yankin ya tabbatar da cewa, jiragen sun jefa bama-bamai tare da lalata sansanoni da rumbun adana kayayyaki na ‘yan ta’addar.
“An kai harin bama-bamai da jiragen yakin sojojin suka yi a lokaci guda a Bukar Mairam da Jubularam, Abbaganaram da Chikul Gudu wanda ya yi sanadin tashin bam a rumbun ajiyar mayakan, inda aka kashe ‘yan ta’adda da dama.
“’Yan ta’addan da suka tsira daga fashewar bam a Bukar Mairam da Jubularam sun yi yunkurin tsallaka kogi a cikin gabar tafkin Chadi. Ana cikin haka ne kusan 25 daga cikinsu suka nutse,” inji majiya daga yankin.
Ya ci gaba da cewa, hare-haren ta sama da sojojin suka kai a baya-bayan nan ya yi matukar tasiri ga rundunar ISWAP, tare da dakile shirin kungiyar na kai munanan hare-hare kan sansanonin soji a yankin Arewa maso Gabas.