By Abbas Yakubu Yaura
Wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki kasuwar Pinau dake yankin Pinau a karamar hukumar Wase a jihar Filato, inda suka kashe mutane bakwai tare da jikkata wasu da dama.
Wakilinmu ya ruwaito cewa ‘yan bindigar sun makale ne a yayin da kasuwar ke ci, inda suka ci gaba da tafka ta’asa a yammacin ranar Lahadi.
Jaridar Aminiya a ranar 8 ga watan Disamba, ta ruwaito yadda mazauna wasu kauyukan suka koka kan ‘yan bindiga a wasu kauyukan karamar hukumar Wase.
Mazauna yankin sun kuma yi zargin cewa akwai masu ba da labari a cikin al’ummomin dake aiki tare da ‘yan bindigar.
Shapi’i Sambo, wanda shi ne shugaban matasan Wase, ya tabbatar wa Aminiya harin na baya-bayan nan, inda ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Shugaban matasan ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun kutsa cikin kasuwar inda suka fara harbe-harbe.
Kazalika Wata majiya daga yankin ta shaida wa wakilinmu cewa a cikin kwanaki 10 da suka gabata ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mutane da dama a yankin tare da karbar miliyoyin naira a matsayin kudin fansa.
Sannan yace, “Ana karbar kudin fansa miliyoyin naira daga wajen jama’a. Wani lokaci suna karbar Naira miliyan biyu, wani lokaci kuma Naira miliyan biyar. Kwanaki ukun da suka gabata sun karbi Naira miliyan 5 kafin su sako wani mutum da suka yi garkuwa da shi kwanakin baya.”
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Ubah Gabriel, bai amsa kira da sakon karta kwana ba a lokacin da wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakinsa kan lamarin.