By Abbas Yakubu yaura
Akalla mutane hudu ne suka mutu, yayin da wasu suka samu raunuka a wani hari da aka kai kauyukan Dugara, Daurawa da Gidan Gadi, duk a karamar hukumar Matazu ta jihar Katsina.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 10 na daren Juma’a, kamar yadda mazauna garin suka bayyana.
Wani mazaunin kauyen ‘Yarkirya Usman Ibrahim yace ‘yan bindigar sun mamaye kauyukan da muggan makamai tare da lalata gidaje da dama yayin hare-haren.
Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan jihar Katsina, yace ba su da labarin harin.Sannan yace hakan na iya faruwa ne sakamakon rashin tsarin sadarwa a yankin da lamarin ya faru.
Isah ya bada tabbacin zai yiwa jama’a bayanin gaskiya ko akasin haka da zarar ya tabbatar.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa jihar Katsina dai na daya daga cikin jihohin da ‘yan fashin suka addaba lamarin daya tilastawa dubban mutane kaurace wa kauyukansu.
A ranar Litinin din data gabata ne wasu ‘yan bindiga suka yi awon gaba da hakimin kauyen Fankama, Ahmed Saidu, da matarsa, da wasu mutanen kauyen da dama.