Mutane 6 ne aka kashe tare da kona gidaje a wani kazamin harin da wasu da ake kyautata zaton ‘yan kungiyar Al-Shabaab ne suka kai ranar Litinin a yankin gabar tekun Kenya da ke kan iyaka da Somaliya, in ji jami’an ‘yan sanda da gwamnati.
‘Yan sanda sun ce an fille kan mutum daya tare da harbe wasu biyar ko kuma aka kona su a wani kauye da ke gundumar Lamu mai tazarar kilomita 420 daga kudu maso gabashin Nairobi.
Kwamishinan gundumar Lamu Irungu Macharia ya ce maharan da ake zargin mayakan jihadi ne daga kungiyar Al-Shabaab mai alaka da Al-Qaeda da ke kan iyaka da Somaliya.
“Jami’an tsaron mu suna bin su, kuma muna neman goyon baya daga mutanen yankin don taimaka mana saboda idan muka yi aiki tare muna samun nasara,” kamar yadda ya shaida wa AFP.
‘Yan sandan sun ce maharan sun daba wa wani dattijon garin wuka tare da fille kai tare da kona gidansa, sannan suka harbe wani mutum da aka tsinci gawarsa a bakin titi.
An gano gawarwakin wasu mutane hudu da suka kone ba za a iya gane su ba tare da daure hannayensu a wani wurin, kamar yadda rahoton ‘yan sandan da AFP ya gani ya nuna.
“Haka kuma an kona gidaje da dama a cikin unguwar tare da kona dukiyoyin da ba a san kimar darajar kudin su ba,” in ji rahoton.
An gano harsasai kuma ana ci gaba da gudanar da bincike.