Mutane 11 da suka hada da fararen hula hudu ne aka kashe a wani yunkurin juyin mulki da aka yi wa shugaban kasar Guinea-Bissau Umaro Sissoco Embalo, kamar yadda kakakin gwamnatin kasar Fernando Vaz ya fada jiya Laraba.
“Gwamnati ta yi alhinin rasuwar jarumai 11 a lokacin harin. 11 da abin ya rutsa da su – sojoji da jami’an tsaro, da kuma fararen hula hudu da suka hada da wani babban jami’in ma’aikatar noma da direbansa ne suka Mutu a Harin, ” in ji Vaz, wanda kuma shi ne ministan yawon bude ido na yammacin Afirka.
A wani labarin Kuma na daban
An tabbatar da mutuwar mutane tara yayin da wasu shida suka samu raunuka daban-daban a wasu hadurran da suka faru a wurare daban-daban a jihar Ogun ranar Laraba.
Kakakin hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa na jihar, Babatunde Akinbiyi, ya tabbatar da faruwar hatsarin a wata sanarwa daban-daban; da Babban Kwamandan hukumar kiyaye haddura ta tarayya, Ahmed Umar.
Akinbiyi ya ce hatsari hudu sun afku a sassa daban-daban na jihar a ranar Laraba.
A cikin sanarwar, Umar ya ce hatsarin na farko ya faru ne da misalin karfe 6.05 na safiyar ranar Laraba a kusa da Kamfanin CDK da ke Ota a karamar hukumar Ado-Odo-Ota ta jihar.
Ya bayyana cewa, motar dakon mai, wacce ba ta da rijistar lamba, wanda kuma take dauke da man PMS wato man fetur tana kan hanyar Legas zuwa Ibadan ne a lokacin da ta fashe a wasu ‘yan kilomitoci bayan musanyawar da akayi a Sagamu.
Ya ce manya maza takwas, motoci uku, da babur kirar Bajaj ne hatsarin ya rutsa dasu.
Umar ya ce mutane biyu sun mutu, yayin da wasu mutane shida suka fito ba tare da jin rauni ba.
“An ajiye gawarwakin wadanda suka mutu a Idera Morgue, dake Sagamu,” in ji shi.
Akinbiyi ya kara da cewa hatsarin na biyu ya afku ne a kan titin Legas zuwa Ibadan a tsakanin wata babbar mota da ke tsaye da kuma wata tanka mai dauke da man fetur.
Ya ce, motar dakon mai ta rasa yadda za ta yi saboda gudun da ta ke yi, inda ta bi ta kan wata babbar mota da ta yi sanadin tashin gobara, inda ta kashe mutane biyu tare da jikkata wasu biyu.
Kakakin TRACE ya bayyana cewa, hatsarin na uku ya afku ne a daidai titin Legas zuwa Ibadan a wata unguwa bayan wata mota da ta tashi da gudu ta yi karo da wani babur.
Ya kara da cewa hatsarin ya yi sanadiyar mutuwar mutane uku, daya kuma ya jikkata.
Akinbiyi ya bayyana cewa hatsarin na hudu ya afku ne a gadar Olomore da ke Abeokuta lokacin da direban ya yi barci kuma ya rasa yadda zai yi ayayin da yake tsaka da tuki.